Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa, alhakin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ya rataya ne akan gwamnatin tarayya da gwamnonin jihohi.
Da yake magana yayin ganawarsa da kungiyar gwamnonin Nijeriya (NGF) a gidansa da ke Legas a ranar Talata, shugaban, a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale, ya fitar, ya sake yin Allah-wadai da kashe-kashen da aka yi a jihar Filato.
- Bikin Kirsimeti: Tinubu Ya Yi Allah-wadai Da Hare-haren Filato
- NAF Ta Lalata Haramtattun Wuraren Tace Mai Guda 6 A Ribas
Da yake jawabi ga gwamnonin, shugaban ya bayar da wani kakkausan umarni ga jami’an tsaro da su dakatar da kashe-kashen da ake yi a jihar Filato tare da kara zage damtse wajen zakulo wadanda suka haddasa munanan abubuwan da suka faru a kananan hukumomin Bokkos da Barkin-Ladi.
Da yake jajanta wa wadanda abin ya shafa, Shugaba Tinubu ya jaddada muhimmancin darajar ran dan Adam inda ya yi kira ga mabiya addinatai mabanbanta da su dinga hakuri da juna domin dorewar rayuwa mai inganci.
“Nijeriya na bukatar zaman lafiya da kwanciyar hankali domin ci gaba, Nijeriya ta mu ce, dole ne mu kula da ita.” Inji Tinubu