Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da fitar da kuɗaɗe domin kafa Cibiyar Yaɗa Labarai ta UNESCO (Media and Information Literacy Institute, MIL) a Nijeriya.
Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a lokacin wani taro da suka yi da Mataimakin Darakta-Janar na UNESCO, Dakta Tawfik Jelassi, a birnin Paris na ƙasar Faransa.
- Google, Microsoft, TikTok Sun Biya Gwamnatin Nijeriya Harajin N2.55trn A 2024 – NITDA
- Xi Ya Aike Da Wasikar Taya Murna Ga Taron Fahimtar Kasar Sin
Idris, wanda ya bayyana hakan a gefen ziyarar da Shugaba Tinubu ya kai ƙasar Faransa, ya bayyana irin goyon bayan da Shugaban Ƙasar ke bai wa aikin.
Ya ce:“Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da goyon baya sosai ga aikin, kuma ya amince da fitar da duk wasu kuɗaɗen da ake buƙata domin cibiyar ta fara aiki nan take, wadda za ta kasance a Babban Birnin Tarayya.”
Ministan ya nuna jin daɗin sa ga UNESCO da ta bai wa Nijeriya haƙƙin kafa Cibiyar ta MIL, wadda ita ce kaɗai irin ta a duniya.
Ya tuna ganawar da ya yi da Dakta Jelassi a shekarar 2023, tare da jaddada aniyar Nijeriya na ganin cibiyar ta samu nasara.
Jelassi ya bayyana jin daɗin sa game da kafa cibiyar a Nijeriya tare da nanata muhimmancin sa wajen magance matsalolin da suka haɗa da yaɗa labaran ƙarya, da kalaman ƙiyayya. Ya kuma bayyana ƙoƙarin UNESCO na samar gidan yana mai aminci.
Har ila yau, ya gabatar da shirin UNESCO MIL Cities, wanda ke haɗa ilimin yaɗa labarai a cikin ayyukan birane, waɗanda suka haɗa da harkokin sufuri da al’adu.
Idris ya yi maraba da manufar MIL Cities kuma ya yi alƙawarin cewa Nijeriya za ta taka rawar gani ta hanyar zaɓar wani birni don aiwatar da matakin farko na shirin.
Ministan ya kuma ba da tabbacin cewa Nijeriya za ta yi amfani da ƙa’idojin UNESCO don Gudanar da Kafafen Gidan Yana, wanda ke da nufin inganta tunani da gaskiya tare da kare ‘yancin faɗin albarkacin baki.
Idris ya samu rakiyar Jakadiyar Nijeriya kuma Babbar Wakiliya ga UNESCO, Dr. Hajo Sani, zuwa taron da aka gudanar a hedikwatar UNESCO.