Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan kudirin dokar karin albashi, alawus-alawus na ma’aikatan shari’a a Nijeriya da kuma abubuwan da suka shafi doka.
Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin majalisar dattawa, Sanata Basheer Lado ne ya bayyana hakan a wata sanarwar da ya fitar ranar Talata a Abuja.
- Sin Ta Yi Kira Ga Gamayyar Kasa Da Kasa Da Su Mutunta ’Yancin Kan Sudan Ta Kudu A Lokacin Mulkin Rikon Kwarya
- Shari’a: Ganduje Ya Ki Na’am Da Tayin Jakadanci A Kasashen Afirka
Idan za a iya tunawa manta dai majalisar tarayya ta amince da wani kudirin doka da Shugaba Tinubu ya mika mata na karin albashin alkalan Nijeriya da kashi 300 a watan Yunin wannan shekara.
A cikin sanarwar, Sanata Lado ya siffanta rattaba hannu kan kudirin da shugaban kasar ya yi a matsayin wani gagarumin nasara da ke nuna jajircewarsa na ci gaba da kyautata rayuwar ma’aikatan Nijeriya.
Dan majalisar tarayya ya kuma bukaci alkalan Nijeriya su kara himma wajen ganin an tabbatar da adalci lokacin yanke hukunci.
Sanatan ya ce, “Wannan gagarumin yunkuri na nuna fifikon da shugaban kasa ya ba da muhimmanci ga jin dadin ma’aikatan Nijeriya fiye da komai kamar yadda ya yi a kwanakin baya a taron majalisar zartarwa ta tarayya domin amincewa da sabon kudirin dokar mafi karincin albashi na naira 70. 000.”
Lado ya ce sabuwar dokar ta tanadi albashi, alawus-alawus, da dai sauransu ga alkalai don su nuna sauyin wajen gudanar da ayyukansu, sannan a yi gyara ga wasu masu rike da mukaman siyasa da gwamnati da na bangaren shari’a. Doka mai lamba No. 6, 2002 wacce aka yi wa kwaskwarima ta tanadi hakan ga alkalai.
A cewarsa, daga cikin fitattun abubuwan da dokar ta kunsa sun hada da, “Tsarin biyan albashi, alawus-alawus, da sauran hakkokin alkalai. Gyaran wasu mukaman siyasa da ma’aikatan sashin shari’a da kuma sauran masu da rika da mukamai a bangren ma’aikatan shari’a.