Shugaban kasa Bola Tinubu ya jajanta ma hukumomin sojoji biyo bayan rashin wasu jajirtattun sojoji shida a harin da ‘yan ta’adda suka kai a ranar 4 ga watan Janairun 2025 a wani sansanin soji da ke Sabon Gida a karamar hukumar Damboa ta jihar Borno.
Ya kuma yi kira da a gudanar da cikakken bincike don gano sakacin da ya haifar da mummunan lamarin tare da tabbatar da cewa ya zama darasi mai mahimmanci don hana afkuwar irin wannan a gaba.
- Sukar Gwamnatin Tinubu: Haƙiƙanin Gaskiyar Kama Obi A Abuja
- Yawan Sakwannin Da Sin Ta Yi Jigila a Shekarar 2024 Ya Zarce Biliyan 170
Shugaban, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar, ya jajantawa iyalan sojojin da suka rasu, wadanda sadaukarwarsu ta kare kasa za ta kasance cikin girmamawa da tunawa da su har abada.
Shugaban ya yabawa rundunar sojin kasar bisa gaggarumin daukar matakin da suka dauka, musamman bangaren jiragen sama wajen kaddamar da hare-haren ramuwar gayya. Hare-haren da aka kai ta sama ya yi sanadin kashe ‘yan ta’adda da dama tare da lalata makamai da ababen hawansu yayin da suke yunkurin guduwa.