Shugaba Bola Tinubu ya dawo gida Abuja bayan halartar taron shugabannin kasashen G20 karo na 19 da ya gudana a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil.
Jirgin shugaban kasar ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da misalin karfe 10:20 na dare a jiya Asabar.
- Firaministan Kasar Sin Ya Jagoranci Taron Majalisar Gudanarwar Kasar Sin
- Halartar Shugaba Xi Taron APEC Da G20, Da Ziyarar Aiki A Peru Da Brazil Sun Kasance Wata Hanyar Sada Zumunta Da Hadin Gwiwa
A yayin taron, Tinubu ya amince da shirin kawancen kasashen duniya da zai yi yaki da yunwa da fatara, tare da jaddada muhimmancin manufar ga ci gaban duniya.
A yayin taron, Shugaba Tinubu ya yi amfani da wannan damar wajen halartar rattaba hannu kan takardar amincewa da hannun jarin dala biliyan 2.5 tsakanin Nijeriya da babban kamfanin sarrafa nama na Brazil (JBS S.A.), wanda hakan ke nuni da wani muhimmin mataki na kawancen hadin gwiwar tattalin arzikin kasashen biyu.