Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya gana da tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike da kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa’i, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Sunayen tsoffin gwamonin biyu, na cikin jeren sunayen wadanda za a nada a mukamin minista.
Sai dai, ‘yan majalisar dattawa sun tantance Wike tare da kuma tabbatar da shi, inda kuma suka ki amincewa da El-Rufa’i, sabida rahoton tsaro da aka mikawa majalisar.
Tsaffin gwamnonin biyu, sun isa fadar ta shugaban kasa ne a lokaci daban-daban, inda Wike ya isa fadar da misalin karfe 1:40 na rana, El-Rufa’i kuma ya isa da misalin karfe 2:00 na rana.