A bisa kokarin da ake yi na rage radadin talauci biyo bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi da kuma sake farfado da tattalin arzikin Nijeriya, shugaban kasa Bola Tinubu, ya kaddamar da shirin raba Naira tiriliyan 1.25 ga gidaje miliyan 15.
Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ne ya wakilci Shugaba Tinubu a wajen kaddamarwar wadda ta zo daidai da zagayowar ranar yaki da talauci ta duniya.
- Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace
- Najeriya Ta Yi Imanin Shawarar BRI Za Ta Inganta Ci Gaban Kasashen Afirka
An kaddamar da shirin ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Talata.
Tinubu ya ce, an kaddamar da shirin ne don a tallafa wa marasa karfi a kasar, inda ya ce, taken taron na yakar talauci a duniya: Samar da kyakyawan yanayin aiki da bayar da kariya, ya zo daidai da tsarin shirye-shirye-shiryen gwamnatinsa na sake farfado da fata a zukatan ‘yan Nijeriya.
Kazalika shugaban ya ce, “ Gwamnatinsa zabta shige a gaba domin tabbatar wa daukacin ‘yan Nijeriya, sun samu damar samun walwalar aikin yi da kuma samar musu da kariya. ”
A na ta jawabin a wajen taron, ministar jin kai da yakar talauci Betta Edu, ta jinjinawa shugaban kasa Tinubu kan samar da wannan damar ga ‘yan Nijeriya su miliyan 15.