Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa sama da hanyoyin tarayya 420, gadoji, da sauran ayyukan more rayuwa ko dai an kammala su ko kuma an samu ci gaba sosai a karkashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a cikin shekaru biyun da ta kwashe tana mulki.
Shugaban Kwamitin Ayyuka na Majalisar Dattawa Sanata Barinada Mpigi ne ya bayyana haka a cikin sakon fatan alheri da wakilinsa Ashley Emenike ya gabatar a wajen bikin bude taron Injiniya karo na 33 da Majalisar Dokokin Injiniya a Nijeriya ta shirya ranar Talata a Abuja.
Mai taken “Ci gaban Ingantattun ayyuka na Injiniya da Kasuwanci a Nijeriya: Kwarewa, Biyayya da Rabawa”, taron shekara-shekarar ya jawo kwararru daga ko’ina cikin kasar don yin shawarwari kan dabi’ar injiniya, ka’idojin samar da ababen more rayuwa, da ci gaban kasa.
Mpigi ya yaba da injiniyoyi a matsayin wadanda ba su da makawa sai an sanya su a ci gaban Nijeriya, tare da lura da cewa aikinsu shi ne kashin bayan ci gaban tattalin arzikin kasar, fadada kayayyakin more rayuwa, da ci gaban masana’antu. An kuma bayyana cewa injiniyoyin Nijeriya ba kwararru ba ne kawai, har ma kwararrun masana ne wadanda suka cancanci babban matsayi a cikin tsara manufofi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp