Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Farfesa Yahaya Isa Bunkure a matsayin sabon Shugaban Jami’ar Ilimi Ta Tarayya da ke Zariya (FUEZ), Jihar Kaduna.
Farfesa Bunkure, fitaccen masani ne a fannin koyar da kimiyya, kuma shi ne yake rike da muƙamin Shugaban Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kano a halin yanzu. Sanarwar naɗinsa ta fito ne a ranar Laraba daga mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga.
Jami’ar Tarayya ta Ilimi, Zariya, na daya daga cikin tsofaffin Kwalejojin Ilimi na Tarayya guda huɗu da aka ɗaukaka zuwa matsayin cikakkun jami’o’i a tsakanin shekarar 2022 zuwa 2023. A bisa ga dokokin da suka shafi jagorancin jami’o’i, shugaban jami’a zai yi wa’adin shekaru biyar.
A wani labarin kuma, Shugaba Tinubu ya amince da naɗin wasu muƙamai a fannin ilimi, inda ya naɗa Injiniya Abdurrazaq Abubakar Nakore a matsayin Shugaban Majalisar Gudanarwa na Jami’ar Ilimi ta Tarayya Yusuf Maitama Sule da ke Kano. Har ila yau, ya naɗa Farfesa Abdullahi Tukur Kodage a matsayin sabon shugaban jami’ar.
Nakore, memba ne na ƙungiyar Injiniyoyin Nijeriya (NSE), kuma ya taɓa rike muƙamin Sakataren Zartarwa na Hukumar Wutar Lantarki a karkara a Jihar Jigawa. Farfesa Kodage kuwa, kwararre ne a fannin ilimi da yake da gogewa a harkar koyarwa da al’amuran gudanarwa.
Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa waɗannan naɗe-naɗen na daga cikin ƙoƙarin da gwamnati take yi domin ƙarfafa shugabanci a tsarin ilimi da kuma tabbatar da ingantaccen tsarin tafiyar da sababbin jami’o’in da aka ɗaukaka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp