Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Misis Didi Esther Walson-Jack a matsayin shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya (HoCSF), wacce za ta fara aiki daga ranar 14 ga Agusta, 2024.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale, ya fitar a daren Laraba, an nada Misis Walson-Jack a matsayin babbar sakatariya ta gwamnatin tarayya a shekarar 2017, kuma ta yi aiki a ma’aikatu da dama.
- Shugaba Tinubu Zai Ƙaddamar Da Shirin Lamunin Ɗalibai A Ranar 17 ga Yuli
- Matsalar Tsaro: Ɗalibai Sun Ƙaurace Wa Ɗakunan Kwana A Lakwaja
“Sabuwar shugabar wacce aka nada za ta karbi mukamin ne daga hannun shugabar ma’aikatan gwamnatil Dr. Folasade Yemi-Esan, wacce za ta yi ritaya a ranar 13 ga Agusta, 2024.
“Shugaba Tinubu, yayin da yake gode wa shugabar ma’aikatar mai barin gado bisa aikinta, ya nemi sabuwar shugabar da ta sauke nauyin da ya rataya akanta da gaskiya, da kuma bin ka’idoji na ma’aikatan gwamnatin tarayya,” in ji Ajuri
LEADERSHIP ta rahoto cewa, Didi Walson-Jack ta fito ne daga jihar Bayelsa da ke kudu maso kudancin Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp