Shugaban kasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kan dokar karin albashi da alawus ga ma’aikatan shari’a ta 2024.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, sabuwar dokar ta tanadi karin albashi da alawus-alawus ga ma’aikatan shari’a na kasa.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin majalisar dattawa, Sanata Basheer Lado, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Talata da yamma, ya bayyana cewa, rattaba hannun wani yunkuri na musamman wanda ya nuna jajircewar Tinubu tare da fifita jin dadin ma’aikatan Nijeriya.