Zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tafi birnin Paris na kasar Faransa domin hutawa, yayin da yake jiran ranar bikin rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu.
Daga birnin Paris zai wuce zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da dawafi a dakin Ka’aba.
Wata sanarwa da ta fito daga ofishin mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Tunde Rahman, a ranar Laraba, ta ce Tinubu zai fita ne sabida hutawa daga hayaniyar yakin neman zaben da aka gudanar.
Ya kuma umurci manyan mataimakansa da ma’aikatan yakin neman zabensa su ma su je su dan huta.