Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya taya Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, murnar cika shekaru 58 a duniya.
A wata sanarwa da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Na Musamman Kan Harkokin Yaɗa Labarai, Cif Ajuri Ngelale ya fitar, Tinubu ya ce Idris, gogaggen ma’aikacin gwamnati ne, mawallafi kuma ɗan siyasa, wanda ya kawo ƙwarewa da gogewa sosai ga matsayin sa na Ministan Yaɗa Labarai Da da Wayar Da Kai.
- Tinubu Zai Kaddamar Da Motoci 2,700 Masu Amfani Da Iskar Gas A Watan Mayu
- Real Madrid Na Taimakawa Benzema Domin Murmurewa Daga Raunin Da Yake Fama Da Shi
Ya ce: “Alhaji Idris ya kasance a sahun gaba a harkar yaɗa labarai da hulɗa da jama’a a matsayin sa na wanda assasa, kuma Shugaba, sannan Mawallafi na jaridar Blueprint; kuma a matsayin sa na Shugaban Rukunin Kamfanonin Bifocal, mai ba da shawara kan hulɗa da jama’a, da Kings Broadcasting Limited, wanda ke da gidan rediyo da aiki a Abuja kan mita 106.5 zangon FM.
“Matsayin sa na Babban Sakataren Ƙungiyar Mamallakan Jaridu ta Nijeriya (NPAN) kafin a naɗa shi minista ya nuna ƙwazo da gudunmawar da ya ke bayarwa a fagen yaɗa labarai a Nijeriya.”
Shugaban Ƙasar ya yaba wa ministan bisa jajircewar sa da kuma irin rawar da ya ke takawa wajen samun daidaito.
Ya yi wa ministan fatan ƙarin shekaru masu yawa cikin ƙoshin lafiya da kuma samun nasarar hidimar da ya ke yi wa ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp