Shugaba Bola Tinubu ya bayyana alhininsa game da rasuwar Alhaji Abbas Sanusi, Galadiman Kano kuma babban mai nada sarki a masarautar Kano.
Ya rasu yana da shekara 92 bayan doguwar jinya. Ya bar ‘ya’ya da jikoki da dama.
- Mamakon Ruwan Sama: Matafiya sun Maƙale a Taraba Sakamakon Ɓallewar Gada
- Obasanjo Zai Zuba Jarin Dala Miliyan 700 A Kamaru
Daga cikin ‘ya’yansa akwai Alhaji Abdullahi Abbas, shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano.
Shugaba Tinubu, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, ya bayyana marigayin a matsayin babban ginshikin masarauta kuma mai neman ci gabanta.
Shugaba Tinubu ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Kano da majalisar masarautar Kano da kuma iyalan marigayin bisa wannan rashi mara misaltuwa.
Shugaban ya yi addu’ar Allah ya sa Jannatul Firdaus, ta zama makoma ga Galadima.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp