Shugaba Bola Tinubu ya yi wa sabbin Shugabannin Sojoji ado da karin girma domin su dace da sabbin muƙamansu.
Sabbin shugabannin rundunar sojin kasar da aka yi wa ado sun hada da Laftanar Janar, wanda yanzu ya zama Janar Olufemi Olatubosun Oluyede, a matsayin Babban Hafsan Tsaro (CDS); da kuma Manjo Janar yanzu ya koma Laftanar Janar Emmanuel Undiendeye Undiendeye a matsayin Babban Hafsan Tsaro na farin kaya (CDI).
- Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai
- Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda
Sauran su ne Manjo Janar, wanda yanzu ya zama Laftanar Janar Waidi Shaibu a matsayin Babban Hafsan Soja (COAS); Air Vice Marshal, wanda yanzu ya zama Air Marshal Kevin Aneke a matsayin Babban Hafsan Sojan Sama; da kuma Rear Admiral, wanda yanzu ya zama Vice Admiral Idi Abbas a matsayin Babban Hafsan Sojan Ruwa.
Shugaba Tinubu ya sanar da maye gurbin Shugabannin Rundunar tsaron ne a ranar Juma’ar da ta gabata, wani mataki da aka danganta da bukatar sake mai da hankali da kuma karfafa tsaron kasa.
Bayan haka, Shugaba Tinubu ya bukaci sabbin Shugabannin Rundunar tsaron da su dauki mataki mai tsauri kan barazanar tsaro da ke tasowa a fadin kasar, yana mai gargadin cewa ‘yan Nijeriya na tsammanin ganin sakamako, ba uzuri ba.














