Shugaba Bola Tinubu na shirin karfafa dangantakar tattalin arziki da siyasa tsakanin Nijeriya da kasashen Larabawa a cikin wannan mako a yayin wani taron kasashen Saudiyya da Afirka da kuma Larabawa da za a yi a kasar Saudiyya.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar shugaban kasa a ranar Lahadi a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
- Jiragin Sama Ya Yi Hatsari Dauke Da Ministan Tinubu Na Wutar Lantarki A Ibadan
- An Kammala Bikin Canton Fair Tare Da Kulla Yarjeniyoyin Da Suka Kai Dala Biliyan 22.3 A Zahiri
A cewarsa, Tinubu zai halarci taron koli na Saudiyya da Afirka da kuma taron kasashen Larabawa da kasashen Afirka da za a yi a ranar 10 da 11 ga watan Nuwamba, 2023 a birnin Riyadh, a kokarinsa na kara jawo masu saka jari daga kasashen waje (FDI) da hadin guiwar kasuwanci daga kasashen Larabawa zuwa Nijeriya da Afirka.
Mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai ya ce, Tinubu zai tattauna batutuwan da suka shafi kasuwanci, yaki da ta’addanci, noma, samar da ababen more rayuwa da kuma batutuwan da suka shafi muhalli yayin ganawa da Saudiyya da wasu shugabannin kasashen Larabawa.