Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, zai bar Birnin Tarayya Abuja zuwa Birtaniya don fara hutun mako biyu a wani bangare na hutun shekara.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga, ya fitar.
- Ndume Ya Bukaci Tinubu Ya Dauko Sojojin Haya Don Yakar ‘Yan Ta’adda
- Jirgin Ruwa Dauke Da ‘Yan Maulidi 200 Ya Nutse A Neja
Ya shaida cewa shugaba Tinubu, zai yi amfani da mako biyun a matsayin hutun aiki da kuma yin tunani kan sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatinsa.
Ana sa ran shugaba Tinubu zai dawo Nijeriya da zarar hutun ya kare.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp