A wani wasa mai ban sha’awa da suka buga a filin wasa na Muhammad Dikko da ke birnin Katsina a ranar Asabar, kungiyar kwallon kafa ta Niger Tornadoes ta doke abokiyar karawarta Kano Pillars a wasa na farko da sabon kocin Pillars Babaganaru ya buga, wasan ya tashi da ci 2-0.
Kungiyar Tornadoes ta jefa kwallayenta biyu bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Dabai ne ya zura kwallon farko a minti na 58 kafin Shimagande ya tabbatar da nasarar da ci biyu a minti na 88, wanda hakan ya tabbatar da nasarar bakin.
Sabon Kocin Kano Pillars Babaganaru na fatan ganin ya Dawo da martabar Pillars a harkar kwallon kafa a Nijeriya, Pillars ta sallami tsohon kocinta bayan da ta sha kashi a hannun Barau Fc a wasan Mako na 9 da suka buga a makon da ya gabata, inda kuma nan take ta sanar da nadin Babaganaru a matsayin sabon kocin kungiyar.
Wannan nasara mai ban mamaki ta sa kungiyar Niger Tornadoes ta koma matsayi na biyu a teburin gasar, inda yanzu take da maki 17 a kasan Nasarawa United. Hakazalika, sakamakon ya bar Kano Pillars a cikin mawuyacin hali a gasar yayin da ta ke matsayi na 19 da maki 8 kacal.













