Tottenham ta kammala sayen ɗan wasan tsakiyar ƙasar Holland, Xavi Simons, daga RB Leipzig kan kuɗin fam miliyan 51.8 (€60m).
Ɗan wasan mai shekaru 22 ya ce tun da daɗewa yake mafarkin wannan dama, bayan ya kammala gwajin lafiya a kulob ɗin da Thomas Frank ke jagoranta.
- Akwai Bukatar Gwamnonin Arewa Su Yi Koyi Da Jihar Legas Wajen Bunkasa Albarkatun Fatu
- Sin: Shawarar Gina Kyakkyawar Makomar Bil Adam Ta Bai Daya Ta Samu Amincewa A Duniya
Simons ya buga wasanni 78 a Leipzig, inda ya zura ƙwallaye 22 tare da taimakawa aka ci ƙwallaye 24.
Ya dawo Leipzig ne a matsayin aro daga PSG a 2023, kafin ya sanya hannu kan kwantiragi a farkon wannan shekara.
Haka kuma ya buga wasanni 28 tare da ƙasar Holland, inda ya ci ƙwallaye biyar, tun bayan gasar cin kofin duniya a Qatar 2022.
“Tottenham babbar ƙungiya ce, kuma tun lokacin da na haɗu da kocin, na fahimci wannan shi ne wurin da ya dace a gare ni,” in ji Simons, wanda aka dade ana dangantawa da komawa Chelsea.
Kocin Tottenham, Frank, ya bayyana cewa Simons ya rattaba hannu kan yarjejeniya mai tsawo, kuma babban abin da kulob ɗin ke nema ne saboda duk da ƙarancin shekarunsa, ya riga ya samu gogewa sosai.
Simons shi ne na uku da Tottenham ta dauko a bana bayan Joao Palhinha da Mohammed Kudus. A da Chelsea ta yi tattaunawa da Leipzig domin daukarsa, amma daga baya ta janye saboda tana kokarin kammala cinikin Alejandro Garnacho daga Manchester United akan fam miliyan 40.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp