Kamuwa da rashin lafiya a Nijeriya ya zama kalubalen da za a iya cewa ruwan dare, amma samun jinya da magani kuma sai su zama babban kakanikayi sakamakon tsadar magunguna da ‘yan Nijeriya da dama ba su iya saye.
Tsadar magungunan musamman wadanda ake amfani da su yau da gobe irinsu rigakafi, maganin suga, ciwon kai, mura, maleriya da sauran cutukan da jama’a ke yawan fama da su na yau da kullum, abun da kawai majinyatan ke iyawa shi ne tururuwa zuwa asibitoci domin neman waraka.
- Gwamnatin Zamfara Zata Raba Dabbobi Kyauta Ga Mata
- Gwamnatin Zamfara Zata Raba Dabbobi Kyauta Ga Mata
Tsadar kayan magunguna babban barazana ne da ke fuskantar yawaitan zuwa asibitoci domin neman jinya, lamarin da ke neman a gaggauta daukan matakin shawo kansa domin kauce wa yawaitar mace-macen majinyata sakamakon rashin kudi ko kasa sayen magunguna.
Majinyata da dama sun nuna halin da suke ciki na mawuyacin yanayi musamman wadanda suke fama da karamin karfi kuma ba su cikin shirin inshuran kiwon lafiya, kamar wata uwa, Idowu Akinyemi wacce take fama da ciwon suga, ta shiga mamaki lokacin da ta je sayen magungunanta bisa gano yadda maganin ya yi tashin gwauron zabi farad daya.
“Lokacin da na sayi maganina na karshe shi ne, naira dubu 3,000, amma yanzu maganin da na je shagon sayar da magunguna ya kai naira 5,000,” Idowu ta nuna damuwarta kan tashin magungunan.
Dokun Bolarinwa, mai fama da ciwon hawan jini, ya ce, yana kan magani da jinya a kowani lokaci, amma tsadar magungunan sannu a hankali ya sanya shi kauce wa ka’ida da dokokin da likita ta dora shi a kai.
“Ni tsohon ma’aikaci ne ba na da wata hanyar samun kudi a kowani lokaci. ‘Yan shekaru, ina ta fama da jinyar da ke damuna tare da gudunmawar ahlina, amma a ‘yan kwanakin nan gaskiya lamuran sun mana wuya. Na koma tsallake ranakun shan magani domin ba mu iya sayen maganin a kowani lokaci.”
Ade Ogun, wanda ya sayo maganinsa, sai dai ransa a bace cikin damuwa yayin da ya gano cewa maganin da yake amfani da shi ya tashi, “Na sayi maganina a baya kan kudi naira 500, amma da na koma ya tashi da kaso 100, na yi matukar mamakin tashin maganin har haka,” Ade ya shaida.
Funmi Olaoye, matar aure ce wacce uwa ce kuma, da take jinyar danta mai fama da ciwon Asma, ta ce, “Yarona yana matukar bukatar kulawar magani kan ciwon asma da yake fama da shi, amma ba na iya sayen rashin maganin da ya dace na saya saboda tsada,” ta koka.