A ranar Talata ne gwamnatin jihar Kogi ta fara rabon buhunan shinkafa Tirela 50 ga marasa karfi a matsayin tallafi don rage wahalhalun da al’ummar jihar ke ciki.
Da yake jawabi yayin rabon kayan abincin a dandalin Muhammadu Buhari da ke Lokoja, Gwamna Ahmed Ododo ya gargadi jami’ai da su guji karkatarwa ko boye kayayyakin tallafin.
- Tsadar Rayuwa: Yadda Aka Kama Manyan Motoci 4 Na Kayan Abinci A Jigawa
- Gwamnatin Katsina Za Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Aiwatar Da Dokar Hana Boye Hatsi Da Tsadar Haya
Gwamnan ya ce, tallafin an yi shi ne da nufin tallafawa marasa karfi na matakin karshe don rage musu tsadar rayuwa da ake fuskanta a halin yanzu.
An bayyana cewa, za a raba shinkafar ne a unguwanni 239 da ke fadin kananan hukumomi 21 na jihar.