Asusun ba da lamuni na duniya, IMF ya bukaci gwamnatin tarayya da ta daina bayar da tallafin wutar lantarki gaba daya a Nijeriya sakamakon halin kuncin da ‘yan Nijeriya ke ciki tun bayan cire tallafin mai a watan Mayun 2023.
Cibiyar Bretton Woods ce ta bayar da wannan shawarar a matsayin hanyar da Nijeriya za ta bi domin habaka fannin tattalin arziki duba da yadda aka kashe sama da biliyan Naira biliyan 375.8 a waccar shekarar kan tallafin.
- Mata Mu Kara Hakuri A Zamantakewar Aure -Aisha Seyoji
- Hukumar Karɓar Ƙorafi Da Yaƙi Da Rashawa Ta Kwace Rumbuna 10 Da Aka Ɓoye Abinci A Kano
A cewar rahoton ‘Post Financing Assessment (PFA)’ da aka buga, IMF ta kara da cewa, gwamnatin tarayya ta aiwatar da shirin na cire tallafin wutar lantarki baki daya.
IMF ta yabawa gwamnatin tarayya kan sauye-sauyen da ta aiwatar zuwa yanzu amma ta sake nanata cewa, a cire tallafin man fetur da wutar lantarki.