Kungiyoyin kwadago ta kasa (NLC) reshen jihar Adamawa ta bi sahun mambobin kungiyar a kasa baki-daya, wajan shiga zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin tarayya, tare da kira ga gwamnatin da ta duba yanayin da talakawar kasar ke ciki.
Kwamared Emmanuel Fashe, shi ne shugaban kungiyar ya yi kiran a Yola, ya ce gwamnatin tarayya ta sassauta manufofinta, domin kuwa ‘yan Nijeriya na cikin wahalar da ba za’a iya kwatantashi ba.
- Tsadar Rayuwa: Zanga-zangar NLC Ta Mamaye Abuja, Legas, Gombe, Oyo, Ondo, Ribas Da Sauran Jihohi.
- Shirin Yaƙi Da Talauci: Mun Yi Wa Ƙananan Masana’antu 7,000 Rijista A Adamawa – Bawa
Da yake karbar wasika a madadin gwamnatin jihar, shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Dakta Edgar Amos Sunday, ya bada tabbacin ma’aikatan na yin duk mai yiwuwa don ganin an magance wahalhalun da al’ummar jihar Adamawa ke ciki.
Shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin ya kuma yabawa kungiyar kwadagon bisa yadda su ka gudanar da zanga-zangar bisa tsari, kwanciyar hankali da lumana.