Rundunar ‘yansandan jihar Neja ta kama wasu mutane 25 da ake zargi da hannu a zanga-zangar adawa da yunwa da tsadar rayuwa da aka yi a ranar Litinin a Minna, babban birnin jihar.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yansanda (PPRO), SP Wasiu Abiodun ne ya tabbatar da cewa, wata Aisha Jibrin ce jagora wacce itace ta haddasa zanga-zangar, kuma an kama ta tare da wasu mutane 24 da ake zargi.
- Tsadar Rayuwa: Majalisar Wakilai Ta Nemi Gwamnatin Tarayya Ta Lalubo Mafita
- Muhimmiyar Kalmar Dake Shafar Sin: Sabon Karfin Neman Bunkasuwa
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, wasu mata da matasa masu yawa a ranar Litinin din da ta gabata sun fito kan titi inda suka tare hanyar Kpagungu ta hanyar Minna zuwa Bida a babban birnin jihar Neja, inda suka yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da yunwa da tsadar rayuwa.
Matan dauke da alluna da rubuce-rubuce akai wanda ke cewa “Ba abinci, yunwa na kashe mu” sun bukaci a samar da ingantaccen tsarin rayuwa tare da rage tsadar rayuwa ga ‘yan kasar.
Sun zargi masu rike da mukaman siyasa da rashin kula da halin da suke ciki. Inda suka ce da kyar suke cin abinci a rana sau daya.
Zanga-zangar ta haifar da cunkoson ababen hawa a hanyar Minna zuwa Bida, wadda ta kasance hanyar da ta hada yankin Kudu-maso-Yamma na kasar nan daga Arewa ta Tsakiya.