A yayin da dokar hana yin Acaba, da aka fi sani da Okada ta fara aiki a ranar Laraba a jihar Legas, an wayi gari babu ‘yan Acaba akan titi.
Sai dai a kowacce doka in ance eh sai wasu sun ce A’a. An samu wasu ‘yan okada da suka bijirewa dokar hana zirga-zirgar, bayan da hukuma ta musu tara-tara, wasu sun sun shiga Hannun hukumar su da baburan su yayin da sauran suka tsere suka bar baburan.
Shugaban rundunar kula da bin doka da oda ta ‘yan sandan jihar Legas, CSP Shola Jejeloye, ya tabbatar da cewa mahayan sun bi kuma sun yarda da dokar duk da cewa an kama babura 46 da safe yayin da wasu 34 kuma aka kama su da yamma.
Ya kuma ce an kama ‘yan okada 13.
Gwamnatin jihar dai ta haramta aikin Okada a kananan hukumomi shida acikin unguwanni tara dake karkashinsu.
Kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Ikeja, Surulere, Eti-Osa, Legas Mainland, Legas Island da Apapa.