A siyasance, kowa yana so a ce shi ne babba, inda jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya fito fili ya nuna cewa shi ne babba a tsakaninsa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a 2023, Mista Peter Obi.
Wannan takaddama ta kunno kai ne tun lokacin da wasu masu ruwa da tsaki suka bukaci Kwankwaso ya amince da shirinsu na zama a abokin takarar Obi a zaben shugaban kasa a 2027.
- Hadarin Kwale-kwale A Kaiama: Gwamnan Jihar Kwara Ya Bayar Da Tallafin Naira Miliyan 100
- Matasa 3 Sun Shiga Hannu Kan Kashe Wani Mutum Don Mallakar Filinsa A Kano
Tsohon gwamnan Jihar Kano, wanda kuma shi ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, ya ce yana jira ya ga ka’idojin da za a yi amfani da su wajen gudanar da irin wannan tsarin, duba da irin iliminsa da siyasa a kan Obi.
A wani faifan bidiyo da ya yi ta yawo a kafafen sada zumunta a ranar Asabar, an ga Kwankwaso na bayyana cewa, “Na fi Peter Obi girma a siyasance. Ni babban yayansa ne. Ina da kwarewa fiye da shi. Na yi kokari fiye da shi lokacin da nake gwamnan jihata.
“Ba ni da matsala wajen zama mataimakin takarar Peter Obi, amma sai dai idan an cika wasu sharudda,” in ji shi, yana mai jaddada cewa duk wani kawancen da za a iya kullawa dole ne a gina shi bisa amana.
Ya kara da cewa, “A shirye muke mu tattaunawa, muddin aka amince da sharuddanmu,” in ji shi, wanda ke nuna cewa shi da Obi a shirye suke su kulla kawancen siyasa da shugabancin jam’iyyar LP a gabanin zaben 2027.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa Obi ne ya zo na uku a zaben da ya gabata da kuri’u 6,101,533, yayin da Kwankwaso ya taka rawar gani a jiharsa ta Kano, ya samu kuri’u 1,496,687 a kananan hukumomi 38 daga cikin 44 na jihar.
Kwankwaso ya kuma kasance mai sukar gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu, musamman game da rabon kayan tallafin shinkafa a Jihar Kano. Ya zargi gwamnatin tarayya da kin bai wa gwamnatin jihar tallafin tare da mika wa ga ‘yan jam’iyyar adawa ta APC a jihar.
“Abun takaicin ne yadda gwamnatin tarayya ta raba tallafin shinkafa ga jihohi 35 a hannun gwamnoninsu, in ban da Jihar Kano wanda ak mika kason ga jiga-jigan APC. Wannan babban cin fuska ne ga dimokuradiyyar da kuma tsarin mulkinmu,” in ji Kwankwaso a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Tuwita.
Sai dai kuma, tsohon mai magana da yawun tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya mayar wa da Kwankwaso martini, inda ya bayyana cewa Obi ne babba a siyasance fiye da Kwankwaso.
Ahmad, a cikin wani rubutu a shafinsa na Tuwita, ya ce duk da cewa ya kasance yana girmama Kwankwaso a matsayinsa na dan siyasa mai ci gaba, ba zai iya yin bara’a da furucin nasa ba.
Ya rubuta cewa, “Duk da cewa ban taba zama mai biyayya ga Kwankwasiyya ba, amma a ko da yaushe ina girmama Sanata Rabiu Kwankwaso kuma ina ganinsa a matsayin jiga-jigan dan siyasar da muke da su a kasar nan da ke samun ci gaba.
“Duk da haka, ban yarda da furucin da ya yi kwanan nan ba a lokacin da yake tattaunawa da shi a Kano, inda ya ce ya fi Peter Obi girma a siyasance. Idan aka dubi sakamakon zaben shugaban kasa na 2023, Peter Obi ya samu kuri’u 6,101,533 kuma ya yi nasara a jahohi 11, wanda ke nuna cewa ya samu goyon baya a kasatr nan. Sabanin yadda Sanata Kwankwaso ya samu kuri’u 1,496,687, wanda ya yi nasara a jiha daya kacal, Kano.
“Wadannan alkaluma sun nuna karara cewa, a kalla a yanayin zaben 2023, Peter Obi yana da matukar tasiri a siyasance a fadin kasar nan.
“Don haka Peter Obi ya fi Rabiu Kwankwaso girma a siyasance.”