Shugaban kungiyar masu zabaya reshen Jihar Kaduna, Kwamarde Abubakar Adam ya bayyana cewa, tsananin zafin rana da ke shafar fatar jikin masu zabiya na janyo masu ciwon daji.
Kwamarde Adam ya bayyana hakan a hirararsa da LEADERSHIP Hausa a Kaduna, inda ya yi kira musamman ‘yan siyasa da ke a jihar da su sayawa masu larurar man da suke shafawa don rage radadin na zafin ranar da suke ji a fatar jikinsu.
- Turmutsitsin Rabon Tallafi Da Zakka: Yadda Mutum 10 Suka Rasu A Bauchi Da Nasarawa
- Kungiyar Tsoffin Jami’an NIS Ta Yaba Da Nadin Sabuwar Kwanturola Janar Ta HukumarÂ
A cewarsa, a watannin baya masu larurar uku ne suka rasa rayukansu a Kaduna biyu kuma a karamar hukumar Kajuru da ke a jihar, daya a garin Zariya, saboda tsanin zafin rana da ya janyo masu ciwar daji.
Ya kuma shawarci iyayen yara masu larurar kar su rinka barin ‘ya’yansu na yawan shiga cikin tsananin rana don kar su janyo fatar jikinsu illa, wanda kuma hakan zai iya janyo wa fatar jikinsu cutar daji da kamuwa da sauran cututtukan fata.
Adam ya ci gaba da cewa, kungiyar ta kaddamar da yin gangamin wayar da kan iyayen da ‘ya’yansu ke da larurar kan yadda za su rinka bai wa yaran kariya daga tsananin zafin rana, musamman kan yadda iyayen za su rinka sanya wa ‘ya’yansu kayan da za su kare jikinsu daga zafin rana.
Shugaban ya kara da cewa, cutar dajin babban kalubale ne ga rayuwar masu larurar.