Rahotanni daga ofishin kula da tsarin ba da jagoranci ga taswirar tauraron dan Adam na kasar Sin a jiya Lahadi, tun bayan da aka kammala tsarin Beidou-3 da aka fara aiki da shi a shekarar 2020, tsarin ya ci gaba da gudanar da ayyukansa cikin aminci yadda ya kamata, kuma ya ci gaba da samar da hidimomi na taswirar tauraron dan adam mai karfin gaske. A halin yanzu, tsarin Beidou yana ba da hidima ga sanaoi daban daban, ya zama muhimmin abu wajen inganta ci gaban tattalin arzikin alumma.
Daga bisani, yayin da aka inganta ci gaba kasuwanci da masanaantu da amfani da tsarin Beidou a duniya baki daya, tsarin Beidou zai bunkasa wani nau’i na jagorancin taswira, kuma nan da shekara ta 2035, za a gina wani sabon nauin tsarin da babu kamarsa, da zai kunshi kowa, mafi kwarewan tsarin lokaci na sararin samaniya dake zama tushen. (Safiyah Ma)