Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya ce tsarin kawance na kungiyar “BRICS +” ya samar da wani sabon dandalin hadin gwiwa ga kasashe masu tasowa tare da taimakawa wajen inganta hadin kai a tsakaninsu.
Wang Wenbin, ya bayyana yayin taron manema labarai na yau Alhamis cewa, kasar Sin ce ke rike da shugbancin kungiyar BRICS a bana. Kuma tun daga farkon banan, kasar ta yi aiki tukuru wajen ganin ta kammala ayyuanta a matsayin shugabar kungiyar, haka kuma ta yi duk wani kokari na inganta hadin kai a bangarori daban daban, tare da karbar bakuncin taruka da shirye-shirye kusan 130. A lokaci guda kuma, kasar Sin ta yi matukar kokarin inganta hadin gwiwar kungiyar da zurfafa tsarin hadin gwiwa na “BRICS +”, tare da karfafawa karin kasashe masu tasowa gwiwar shiga a dama da su yadda ya kamata a cikin kawancen kungiyar. (Fa’iza Mustapha)