A baya bayan nan aka rufe bikin baje kolin samar da kayayyaki na kasa da kasa karo na uku a birnin Beijing. Bikin na wannan karo ya samu halatar kamfanoni guda 1200, cikinsu adadin kamfanonin Amurka ya karu da kaso 15 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin a bara, wanda ya kasance gaba cikin kamfanonin kasashen ketare da suka halarci bikin. Haka kuma, an kulla yarjejeniyoyi da shirye-shiryen hadin gwiwa sama da dubu 6 yayin biki na wannan karo.
Kyawawan sakamakon da aka samu a bikin ya nuna bukatun al’ummomin kasa da kasa na tabbatar da ingancin aikin samar da kayayyaki a tsakanin kasa da kasa. A hakika dai, ba za a iya maye gurbin tsarin samar da kayayyaki na kasar Sin a duniya ba, ganin yadda yake da saurin gudanar da ayyuka, da tsimin kudade, da kuma yin kirkire-kirkire.
A matsayin kasa daya kadai da take da dukkan fannonin masana’antu da MDD ta tanada, kasar Sin tana iya taimaka wa kamfanoni wajen samar da kayayyakin da suke bukata cikin sauri. Kana, tsarin samar da kayayyaki ya samu kyautatuwa a fannin tsimin kudade sakamakon bunkasuwar fasahar sadarwa. Haka zalika, kasar Sin na ci gaba da kyautata yanayin kasuwanci a cikin gida, ta hanyoyin gabatar da jerin manufofin samar da sauki ga kamfanoni, da inganta aikin ba da hidima, da kuma takaita ayyukan da abin ya shafa da dai sauransu, lamarin da ya taimaka wa bunkasuwar kamfanonin kasashen waje dake kasar Sin.
Ban da haka kuma, yadda kasar Sin take karfafa yin kirkire-kirkire bisa bunkasuwar fasahar AI, ya samar da damammaki ga kamfanonin ketare wajen neman sabbin ci gaba. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp