Abokai, yanzu haka kasar Sin tana gudanar da babban taron wakilan jami’iyyar kwaminis da ke kan karagar mulkin kasar karo na 20, inda ake fatan gabatar da taswirar bunkasuwar Sin a nan gaba.
A rahoton da babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kana shugaban kasar Xi Jinping ya gabatar a gun taron, ya sake nanata muhimmancin gaggauta raya aikin noma. Yau “duniya a zanen MINA” zai bayyana muku muhimmancin tsarin zamanintar da aikin noma a Sin ga bunkasuwar duniya.
Injuna biyu na zamani da na zana, su ne babbar motar aikin gona maras matuki da karamin jirgin saman aikin gona maras matuki da Sin ta kera. Dukkansu na iya gudanar da aikin noma iri daban-daban ba tare da ma’aikata da dama ba.
Sin ta fito da wata managarciyar hanya da ta dace da halin da take ciki ta zamanintar da aikin noma bisa kimiyya da fasaha na zamani. Daga cikinsu, injunan aikin noma na zamani, ya ciyar da wannan aiki gaba.
Alkaluman kididdiga na nuna cewa, yawan kudaden dake shafar kasuwar sai dai injunan aikin noma, ya kai RMB Yuan biliyan 531, wanda ya karu da kashi 6.6% bisa makamancin lokaci na bara. Kana kasar tana fitar da injunan zuwa sassan duniya.
Darektan cibiyar nazarin tsare-tsaren siyasa da tattalin arziki na kasar Armenia, mista Benjamin Pogo ya ce, rahoton da mista Xi Jinping ya gabatar a gun taron ya nuna cewa, kasar Sin ta gabatar da shawarar raya kasashen duniya da ma shawarar kiyaye tsaron duniya, wadanda take son aiwatarwa tare da kasa da kasa.
Ya ce, “Wadannan shawarwari sun bayyana fatan kasar Sin na cin moriya da samun bunkasuwa tare da ragowar kasashen duniya, kuma ya kasance babbar gudunmawar da ta bayar wajen magance kalubaloli da Bil Adama ke fuskanta, da ma ingiza ci gaban wayin kai da al’adun Bil Adama.”
A takaice, kasar Sin ta tsara managarciyar hanyar da ta dace da halin da take ciki na zamanintar da aikin noma bisa hanyoyi na kimiyya da fasahohi na zamani. Ban da wannan kuma, manufar bude kofa ga kasashen ketare da take aiwatarwa na taimakawa wajen fitar da wadannan injuna da fasahohi zuwa ketare.
Bunkasuwar al’umma ta ta’allaka da tsaron hatsi, kuma tabbatar da samar da isashen hatsi na da babbar ma’ana ga raya kasa mai wadata.
Ko shakka babu, bisa shawarar raya duniya baki daya, yadda kasar Sin ke zamanintar da aikin noma zai samar da gudummawarta wajen warware matsalar karancin hatsi da raya aikin gona, matakin da ko shakka babu, zai baiwa duniya kwarin gwiwa da kuzari wajen tabbatar da samun bunkasuwa. (Mai zane da rubuta: MINA)