Kwanan nan, kasashe masu bin addinin Kirista sun sake yin marhabin da bikinsu mafi kasaita a shekara, wato bikin Kirsimeti. Sanin kowa ne cewa jajebirin bikin Kirsimeti na da ma’anar zaman lafiya da murna. Sai dai a jajebirin bikin na wannan shekara, ba a samu zaman lafiya ba, inda Isra’ila ta kai hare-haren sama ga sansanonin ‘yan gudun hijira da ke tsakiyar zirin Gaza, da ma birnin Khan Younis da ke kudanci, hare-haren da suka halaka mutane a kalla 70.
Yau kusan watanni uku ke nan bayan barkewar rikicin a tsakanin Palasdinu da Isra’ila na wannan karo, wanda ya haifar da hasarar rayukan mutane sama da dubu 20. Duk da cewa akasarin kasashen duniya na yin kira da a tsagaita bude wuta, amma har yanzu kwamitin sulhu na MDD bai kai ga zartas da kudurin tsagaita bude wuta ba, sakamakon yadda wasu kasashe suka hana.
Ban da Gaza, a kasar Ukraine ma, fada na ci gaba, ga shi kuma a Bahar Maliya, yanayin tsaro na tabarbarewa. Sai kuma a kasashen Turai da dama, an tsaurara matakan tsaro a yayin bikin Kirsimeti, don magance faruwar hare-haren ta’addanci…
- Za A Gabatar Da Shirin Gaskiya Na CMG Na “Shekaru 25 Na Sada Zumunta Da Hadin Gwiwa A Tsakanin Sin Da Afirka Ta Kudu”
- An Yi Taron Harkokin Waje Na Kwamitin Kolin Jam’iyyar Kwaminis Ta Kasar Sin
A hakika, babu zaman lafiya a jajebirin bikin Kirsimeti na wannan shekara, haka kuma babu zaman lafiya a duniyarmu. Kuma batun tsaro yana jan hankalin al’ummar kasa da kasa. Muna kuma iya gano haka daga jefa kuri’ar jin ra’ayoyin masu bibiyarmu da muka gudanar ta shafinmu na Facebook a kwanan baya, inda daga kuri’u sama da 1100 da aka kada, kimanin kaso 65% na bayyana “tsaro da kwanciya hankali” a matsayin abin da ya fi jan hankalinsu a shekarar 2023.
Batun tsaro shi ma yana daukar hankalin kasashen yamma, sai dai abin takaici shi ne, suna kauce wa hanyar da ta kamata a wajen tabbatar da tsaro. Domin cimma burin tabbatar da cikakken tsaro, Amurka da sauran kasashen yamma suka ware makudan kudade ta bangaren soja. Daidai dab da bikin Kirsimeti, shugaban kasar Amurka Joe Biden ya sanya hannu a kan shirin kasafin kudin tsaro na shekarar 2024.
Bisa ga shirin, Amurka za ta ware dalar Amurka biliyan 886 ta fannin soja, adadin da ya karu da dala biliyan 30 bisa na shekarar da ta gabata, wanda ya kai wani sabon matsayin koli a tarihinta. Ban da haka, Amurka da sauran kasashen yamma sun kuma kulla kawance-kawance iri iri da sunan “tsaro”.
Duk da kwararan matakan da kasashen suka dauka, amma yanayin tsaronsu sai kara tabarbarewa yake yi a maimakon ingantuwa, shin mene ne dalilin haka?Sabo da tsaron da Amurka da sauran kasashen yamma suke nema shi ne tsaro na kansu, wanda ba shi ne tsaron Bil Adam baki daya ba. Sa’an nan, a yayin da suke zancen kiyaye tsaron duniya, a hakika kiyaye babakeren da suka kafa ne suke magana. Don haka, suka sha kaddamar da yake-yake da kulla kawance da wasu, da ma tada rikici da wasu, kuma hakan ya lalata tsaron kasashen duniya na bai daya.
A hakika, ko a kasashen yamma da kasashen gabas, ko kuma a kasashe masu ci gaba da kuma kasashe masu tasowa, al’ummar kasa da kasa burinsu daya ne, wato a tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasashensu. Abin da kawai ya bambanta shi ne wane irin tsaro ne muke so?
Game da wannan tambaya, kasar Sin ta samar da amsarta bisa shawarar kiyaye tsaro na duniya da ta gabatar, wato Global Security Initiative a Turance, inda ta shawarci kasa da kasa da su yi kokarin tabbatar da tsaronsu na bai daya. Shawarar da kawo yanzu ta samu goyon baya daga kasashe sama da 100. A watan Maris na wannan shekara, kasar Sin ta sa kaimin sassantawa tsakanin Saudiyya da Iran, kuma tun bayan barkewar rikici tsakanin Palasdinu da Isra’ila a watan Oktoba, kasar Sin ta yi ta kokarin sassauta yanayin da ake ciki, da ma samar da sharuddan daidaita batun a siyasance. Baya ga haka, kasar Sin ta sa kaimi ga gudanar da taron zaman lafiya na kasashen kahon Afirka, da shirya taron dandalin Sin da Afirka kan harkokin tsaro. Duk domin aiwatar da shawarar kiyaye tsaron duniya.
Sabo da a ganin kasar Sin, kasashen duniya makomarsu daya ce, kuma babu kasar da za ta iya tsira daga tashe-tashen hankula da ake fuskanta a sassan duniya. Illa dai a hada hannun kasa da kasa wajen kiyaye tsaronsu na bai daya, za a kai ga tabbatar da dauwamammen zaman lafiya da tsaro a duniya.
Sabuwar shekarar 2024 na dab da zuwa, kuma fatanmu shi ne a kara tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniyarmu.