A cikin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14, kasar Sin ta samu ci gaba a bangaren sufurin jiragen kasa na cikin birane, da motocin bas na zirga-zirgar yau da kullum, da zirga-zirga cikin aminci. A halin yanzu, akwai layukan dogo 331 a cikin birane 54 dake fadin kasar, inda jimilar tsawonsu ta kai kusan kilomita 11,000, wanda ke matsayi na farko a duniya.
Babban rukunin gidajen rediyo da talabin na Sin wato CMG, ya samu wannan kididdiga ne daga ma’aikatar kula da sufuri da jigilar kayayyaki ta kasar a kwanan nan.
A yanzu haka, sama da mutane miliyan 200 a kasar Sin sun zabi hanyoyin sufuri masu kiyaye muhalli a kowace rana, wadanda suka hada da miliyan 100 da suke hawa jiragen kasa masu inganci na cikin birane, da miliyan 100 da suke zirga-zirgar ta hanyar bas, da miliyan 24 dake amfani da kekuna. Hanyar sufuri mai kiyaye muhalli ta zama zabi na farko ta zirga-zirgar yau da kullum ga jama’a.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp