Bayanai daga hukumar kula da jiragen kasa ta kasar Sin na nuna cewa, ya zuwa karshen shekarar 2023, tsawon layin dogo na kasar Sin mai saurin tafiya, ya kai kilomita dubu 45.
A cewar wani taron aiki da hukumar ta shirya, gaba daya tsawon layin dogo a kasar, ya kai kilomita dubu 159.
A shekarar 2023, jarin da aka zuba a bangaren layin dogo na kasar, ya kai Yuan biliyan 764.5, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 107.7, karuwar kashi 7.5 bisa 100 kan na makamancin lokacin shekarar 2022. (Mai fassara: Ibrahim)