Tsohon Kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Hon. Yusuf Dahiru Liman, wanda ya wakilci mazabar Makera a majalisar, ya sake lashe kujerarsa a zaben da aka sake a ranar Asabar da ta gabata a mazabu biyar na mazabarsa.
A baya dai Kotun daukaka kara da ke Abuja ta soke zaben Hon. Liman na jam’iyyar APC kan kura-kuran da aka yi a wasu rumfunan zabe, ya kuma ba da umarnin sake gudanar da sabon zabe a wasu mazabun.
- Da Dumi-dumi: Kotun Daukaka Kara Ta Soke Zaben Kakakin Majalisar Kaduna
- Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Bata Da Shirin Tsige El-Rufai – Kakakin Majalisa
Kotun daukaka kara ta bayar da umarnin sake gudanar da zabe a rumfunan zabe guda biyar da ke mazabar biyar biyo bayan karar da dan takarar jam’iyyar PDP, Hon. Solomon Nuhu Katuka da jam’iyyarsa suka shigar.
Tun da farko dai kotun sauraron kararrakin zaben majalisar dokokin jihar Kaduna ta soke zaben Liman a ranar 30 ga watan Satumba tare da ba da umarnin sake zabe a rumfunan zabe 42.
Amma APC da Liman sun shigar da kara kan hukuncin da kotun ta yanke. Hukuncin kotun daukaka kara da Mai shari’a O. O. Adejumo da mai shari’a A.O Oyetula da kuma mai shari’a P. A Obiora suka yi watsi da hukunci farko tare da bayar da umarnin sake gudanar da zabe a mazabu biyar na gundumar Barnawa.
A halin da ake ciki, bayan zaben da aka gudanar a ranar Asabar, Liman na jam’iyyar APC ya yi nasara da kuri’u 18,068, yayin da Nuhu Katuka na PDP ya samu kuri’u 17,404.
Da yake bayyana sakamakon zaben, Baturen zaben, Farfesa Jamilu Ya’u ya ce: “Hon. Dahiru Yusuf Liman bayan ya cika sharuddan doka, an bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara kuma zababben dan majalisar jiha.”