• English
  • Business News
Saturday, October 18, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsige McCarthy Daga Mukaminsa Ya Nuna Me Ake Nufi Da “Dimokradiyyar Amurka”

by CGTN Hausa
2 years ago
McCarthy

A ranar 3 ga watan Oktoba, ‘yan majalisar wakilai da ke karkashin jagorancin jam’iyyar Republican, suka kada kuri’u 216 na amincewa da 210 na kin amincewa don tsige kakakin majalisar Kevin McCarthy daga mukaminsa.

A ranar 1 ga watan Oktoban kowace shekara ne a kan fara gudanar da kasafin kudin gwamnatin tarayyar Amurka.

  • ‘Yan Jarida Sun Yaba Da Ci Gaba Da Al’adun Jihar Xinjiang
  • Gazawar Manyan Kasashe Na Biyan Kudin Memba Ya Sa MDD Ke Fuskantar Karancin Kudaden Gudanarwa

Tun daga watan Satumbar bana, takaddamar da ke tsakanin jam’iyyun siyasa biyu a Amurka game da kasafin kudin sabuwar shekara ke kara kamari. A ranar 30 ga wata, a matsayinsa na kakakin majalisar wakilai, McCarthy ya yanke shawarar hada kai da ‘yan jam’iyyar Democrat, don zartar da kudurin bayar da kudi na wucin gadi. Bugu da kari, kudurin bai hada da shawarwarin masu ra’ayin rikau na jam’iyyar Republican ba, na rage yawan kudin da gwamnatin tarayya ke kashewa da kuma tsaurara matakan kula da iyakokin kasa. Hakan ya kara rura wutar rikicin da ke tsakaninsa da masu ra’ayin rikau a jam’iyyar Republican.

A daren ranar 2 ga watan Oktoban, dan Republican mai ra’ayin rikau wato Matt Gaetz, ya gabatar da kudurin tsige Kevin McCarthy, bisa dalilin dake cewa “Yana hidimtawa jam’iyyar Democrat.”
Jam’iyyar Republican tana da kujeru 221 a majalisar wakilai, wanda ya zarce kujeru 212 na jam’iyyar Democrat. Duk da haka, saboda “tawayen” wasu ‘yan majalisar Republican takwas masu ra’ayin rikau, daga karshe majalisar ta tsige McCarthy.

Kamar yadda manazarta da dama suka yi nuni, adawar da ake yi tsakanin jam’iyyun siyasa a Amurka da kuma yadda ake gwabza fada tsakanin jam’iyyun na daga cikin muhimman dalilan da suka saukar da McCarthy daga mukaminsa. Saboda rikicin jam’iyyun, wasu mambobi masu ra’ayin rikau kadan na iya yin tasiri a kan zaben shugaban majalisar wakilai, wannan alama ce da ke nuna yanayin siyasar Amurka a halin yanzu.

LABARAI MASU NASABA

Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai

Wannan lokacin ne da siyasar Amurka ta yi amfani da muradun son kai na wasu tsirarun mutane, kuma lokaci ne da aka mayar da dimokuradiyyar Amurka matsayin “wasan mulki,” to ta yaya za a iya amincewa da “labarin dimokuradiyya” da ‘yan siyasar Amurka suka rubuta? (Mai fassara: Bilkisu Xin)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103
Daga Birnin Sin

Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

October 18, 2025
Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai

October 18, 2025
Mataimakin Firaministan Sin Ya Zanta Da Sakataren Baitul-mali Da Wakilin Cinikayyar Amurka
Daga Birnin Sin

Mataimakin Firaministan Sin Ya Zanta Da Sakataren Baitul-mali Da Wakilin Cinikayyar Amurka

October 18, 2025
Next Post
Messi

Argentina Ta Gayyaci Messi Buga Mata Wasa Duk Da Raunin Da Ya Samu

LABARAI MASU NASABA

ASUU

Cikin Wata 9 Farfesoshi 309 Sun Bar Aiki A Jami’o’in Gwamnati, In Ji ASUU

October 18, 2025
Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

October 18, 2025
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

October 18, 2025
Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai

Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai

October 18, 2025
Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya

October 18, 2025
Mataimakin Firaministan Sin Ya Zanta Da Sakataren Baitul-mali Da Wakilin Cinikayyar Amurka

Mataimakin Firaministan Sin Ya Zanta Da Sakataren Baitul-mali Da Wakilin Cinikayyar Amurka

October 18, 2025
JIBWIS FCT Ta Yi Taron Yaye Iyaye Mata Da Suka Kammala Koyon Sana’o’i

JIBWIS FCT Ta Yi Taron Yaye Iyaye Mata Da Suka Kammala Koyon Sana’o’i

October 18, 2025
‘Yansanda Sun Cafke Ɓarayi 13 Tare Da Ƙwato Shanu 27 A Kaduna

Gwamnatin Jihar Taraba Ta Ayyana Yi Wa Kasuwannin Sayar Da Dabbobi 9 Garanbawul

October 18, 2025
Iwobi Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Firimiya

Iwobi Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Firimiya

October 18, 2025
Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI

Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.