Shugaban kungiyar tsoffin kansilolin Jam’iyyar APC wanda wasun su suka sauya sheka daga APC zuwa NNPP, sun musanta ikirarin da shugaban Jam’iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas ya yi na cewa, “sun turo su ga gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ne domin su yi musu yakin sunkuru a siyasa da cewa ba gaskiya ba ne, shiftin Gizo ne kawai”.
Shugaban kungiyar, Sunusi Kata Madobi ne ya bayyana hakan yayin wani taron tattaki na musamman da tsoffin kansilloli sama da 3000 suka gudanar cikin ma’aikatar yaɗa labarai da ayyukan cikin gida a sakatariyar Audu Bako a ranar Alhamis.
- Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Jihohin Makwabta, Ya Kara Ta’azzarar Rashin Tsaro A Neja – Bago
- Al Hilal Za Ta Biya Yuro Miliyan 53 Don Ɗaukar Nunez Daga Liverpool
Ya kuma ce, za su sakawa gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da halarci bisa halarcin da ya yi musu na maida su mutane.
Wasu daga cikin tsoffin kansilolin da suka halarci tattakin sun bayyana goyon bayansu ga gwamna Abba Kabir Yusuf.
A nasa jawabin, Dahiru Yusuf daga Gezawa kuma tsohon kansila ya ce, shi ma yana cikin wadanda tsohuwar gwamnatin Ganduje ta hana hakkinsu, don haka maganar Abdullahi Abbas ba gaskiya bane! “Sun ga gwamna Abba zai jikanmu ne shi ne suke neman bata mana ruwa”.
Tun da farko, shugaban tawagar, ya tabbatar da cewa, mai girma Gwamna ya amince zai biya su hakkokinsu wanda gwamnatin baya ta kasa biyansu, kuma yace baya bukatar sakamakon komai daga gare su wai don su koma jam’iyyarsa, ya yi ne domin Allah.
A karshe dubban tsoffin kansillolin wanda suka yi tattaki dauke da kwalaye da rubuntun barranta kansu da Kalaman Shugaban jamiyyar APC na jihar kano, sun kewaya cikin sakatariyar Audu bako zuwa ma’aikatar ƙananan hukumomi domin nuna goyon bayansu ga ayyukan Alherin gwamna Abba Kabir Yusuf
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp