Daga ranar 2 zuwa 4 ga watan Disamban shekarar 2024, an gudanar da taron kasa da kasa na “Fahimtar kasar Sin” a birnin Guangzhou. A yayin taron, fiye da baki 600 na kasar Sin da kasashen waje, ciki har da tsohon firaministan kasar Lebanon Hassan Diab, sun hallara don tattaunawa da yin musayar ra’ayi kan taken “Yin gyare-gyare-zamanintarwa irin ta kasar Sin da sabbin damammakin ci gaban duniya”, inda suka samu ra’ayin bai daya na gudanar da hadin gwiwa. A tattaunawar da ya yi da wakiliyar babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin, wato CMG a takaice, Hassan Diab ya bayyana cewa, fahimtar kasar Sin yana da matukar muhimmanci, domin kasar na bude kofarta ga duniya.
A cikin ‘yan shekarun nan, an samu rashin fahimta, shakku har ma da suka game da ci gaban da kasar Sin ta samu cikin lumana, da tasirinta a duniya. Dangane da haka, Diab ya ce, duk wadannan ba za su hana kasar Sin samun ci gaba a fagen duniya ba. Ya ce, wadanda ba sa son ganin yadda kasar Sin ke kara cimma nasara, suna bukatar karfafa hulda da jama’ar kasar don kara fahimtar kasar. Kuma ya zama dole su amince da gaskiyar cewa kasar Sin ta bunkasa har ta zamanto babbar kasa a duniya a matakai da yawa, kuma kasar Sin na taka muhimmiyar rawa a yayin tabbatar da bunkasuwar kasashe daban daban a duniya. Ya kara da cewa, kamata ya yi su yarda tare da fahimtar hakan cikin natsuwa tare da gina wata gadar tuntubar juna da Sin. (Mai fassara: Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp