Shafin TASKIRA shafi ne da ke zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da; zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da wani sakon wanda muka samu na wata baiwar Allah, inda ta bukaci a tattauna game da yunwar da ake fama da ita a nigeriya, musamman yadda matan aure da ‘yan mata suke ta zinace-zinace dan kawai su ciyar da kansu, da kuma yadda maza suke guduwa suna barin iyalansu cikin yunwa, wasu kuma suna zaune a gida ba tare da sun samu damar fitar ba.
Dalilin hakan ya sa shafin Taskira jin ta bakin wasu daga cikin ma’abota shafin game da wannan batu; Ko me za a akan hakan?, Wane irin kira za a kara yi ga gwamnati da masu hannu da shunu wajen ganin an taimakawa mabukata?, Ko ta wacce hanya ake ganin za a iya shaho kan matsala?.
Ga dai bayanan nasu kamar haka:
Sunana Nabeela Dikko, Daga Jihar Kebbi A Nijeriya:
Babu abin da zamu ce sai Innalillahi wa inna ilaihir raju’un, saboda abin ya wuce misalin da za a misaltawa kowa, ba kowa zai fahimta ba sai wanda rayuwarsa ta tsunduma a cikin wannan halin. Kirana ga gwamnati su kara kokari akan wanda suke yi, su taimaki al’umma mun sani suna iya kokarinsu amma su sani ita yunwa ba tada dadi, mutane na cikin mayuwacin hali, aure yana mutuwa, mutane na mutuwa, zina tayi yawa duk sanadiyar yunwa, abin takaici koda shugabanni sun taimaka amma wanda ake basu wasu basu bari sakon ya isa ga mabukatan, gwamnati na kokari amma abin haushi talakawan tallafi baya zuwa garesu, ya kamata shugabanni sun canja tsarin tallafi sannan a samu masu tsoron Allah a dinga basu ayyukan alheri. Hanya daya ce idan tallafin kudi ne a nemo masu karamin karfi a taimaka masu ko ta hanyar duba act din da ba shi da ko sisi a saka kudin, idan abinci ne a shiga gidaje a rabawa talakawa hannu da hannu. Shawarata ga mata da maza da ku ji tsoron Allah, ku sani karshen wuya dadi kuma wuya bata kashi, maza ayi kokari a sauke hakkin da Allah ya daura musu, mata ku rike mutuncinku, masu kudi aji tsoron Allah ku daina neman mata don ku basu abinci, ayi taimako don Allah kowa ya tuba sannan ya gyara halayensa sannan a nemi sana’a koda karama ce ta fi zaman banza.
Sunana Hafsat Sa’eed, Daga Jihar Kebbi:
To, magana ta gaskiya kam! ana cikin wani yanayi a najeriya dan ba a cewa komai, abun ma har yana neman wuce misali. Gaskiya ya kamata gwamnati ta duba ta kuma tuna alkawarin da ta yi wa al’ummarta don wasu sunanan a cikin kunci wallahi, ni kaina wata kawata dana je na ganta da ‘ya’ya takwas ace kullum sai dai a samu a ci sau daya da kyar in an samu ne fa ake ci sau biyu a rana kuma yara kanana, magana ta gaskiya gwamnati da kuma masu hali su taimaki al’umma. Ni dai a tawa fahimtar gwamnati ita ce za ta iya shawo kan matsalar, domin an ce an sauke dala amman kuma in ka ji yau an ce dala ta sakko gobe ka je siyan wani abun ka ji ta karu, gaskiya gwamnati ta duba ta gyara. Shawarata gare su shi ne duk tsanani yana tare da sauki a yi ta addu’a kuma komai kankantar sana’a ka yi, Allah zai dube ta in sha Allah, Allah ya kaho mana dauki a kasar mu ta najeriys.
Sunana Bilkisu Musa Galadanchi Sokoto Nijeriya:
Wannan wata gagarumar matsala ce dake addabar al’ummar wannan zamanin, sannan kuma laifin hadda rashin bunciken aikin namiji da nasabar halayyarsa kafin a bashi aure, yanada kyau mu sani aure fa idan ka bayar da ‘yarka to wata doguwar tafiya ce da za ta iya turata al’janna ko wuta. To abin da zan ce anan shi ne; gwamnati ta sani talaka sai talaka dan uwansa, masu kudi su sani idan har suna so taimako ya iso ga talakawa sai sun bayar da hannunsu zuwa ga talakan, baiwa masu kudin ta sama yana kawo tabarbarewar kudin kafin ya iso ga talakan, dan duk wani mai ikon saka hannu sai ya yagi rabonsa, amma idan har masu hannu da shuni da gwamnati za su taimaka ne kai tsaye zuwa ga talaka da abin ya zo da sauki sosai. Bincike mai tsayi kafin aure, wane irin miji ‘yata za ta aura?, bangaren gwamnati kuwa samar da aikin yi ga matasa, a bangaren masu kudi kuwa buda kamfuna koda kanana don hakan zai taimaka sosai wurin samuwar ayyuka zai rage zaman banza, su rage siyen kadara suna ajiyewa su mayar da hankali wurin buda masana’antu wurin ganin cewar an rage zauna gari banza. Neman na kai, akwai sana’oin hannu burjik da za ku nema ‘yan mata, zawarawa da kuma matan aure don Allah ku rungumi sana’a gasu nan burjik shi kadai ne, abin da za ku yi ku raba kanku da fadawa halaka ta har abada.
Sunana Hassana Sulaiman (Hassana Hadejia), A Jihar Jigawa:
Kusan maganar gaskiya al’umma na cikin wani hali na tausayi sosai wani sa’in ma sun kai azubar musu da kwalla, dan kuwa hakika za mu iya cewa wasu daga cikin matan na kaiwa kansu inda za su halaka anan duniya da kuma lahiri dan ta dalilin hakan ana iya yi wa wasu matan abin da bai kamata ba, saboda za a basu abinci, sai dai kuma hakan ba hujja ce da mutum zai dogara da ita ba, wai dan yana cikin wani hali ya kai kansa inda zai sabawa mahaliccinsa. To kuma anan kiran da zamu kara jaddawa da farko shi ne; ga malaman addinin isilama da su kara yawaita fadakarwa ga al’umma da basu tarihin rayuwar magabata irin hakurin da suka yi da yunwa da tsangwamar mutane lokacin da suke cikin kunci hakan zai sanya al’umma samun nutsuwa da komawa ga Allah. Sai kuma kiran da za mu yi ga gwamnati anan shi ne; da su samarwa da al’ummar da suka wakilta su wasu hanyoyi na sauki da walwala, da samar da sauyin farashin kayayyakin da ake bukatar sa na yau da kullum musamman ma abinci da sanya wasu mutane da jagoranci na daukan mataki ga duk wani da yaki bin umarnin hukuma da hakan za a iya samun saukin rayuwar, daga karshe kuma ina addu’a ubangiji ya kawo mana saukin rayuwar nan da kawo mana mafita da karshen matsalar tsaro.
Sunana Aminu Adamu Malam Madori A Jahar Jigawa:
To magana ta gaskiya al’umma suna cikin mawuyacin halin rayuwa to, amma ba dalili bane namiji ya gudu ya bar iyalansa koma ya ya zauna a gida ya ki fita nema, domin duk mutumin da Allah ya bawa iyalai to yana buda masa ta hanyoyi da dama domin ya samu damar sauke nauyin iyalansa, kuma su ma matan aure da ‘yan Mata wannan ba zai zama hujjar da za a sabawa Allah ba, domin duk wani abu da za ka samu ta hanyar sabon Allah idan kayi hakuri za ka samu ta hanyar halak, domin hakan kamar jarabawa ce ta rayuwa wanda sai mutum ya dage zai ci wannan jarabawa. To hakika ya kamata gwamnatin kasar mu Najeriya dama gwamnonin jahohi su dauki matakin nema wa al’umma saukin kayan masarufi dama tallafawa al’umma domin samun saukin wannan matsala data dabaibaye al’umma, domin hakan ya jawo masu sun zama mabarata wasu kuma barayi, don haka ya kamata gwamnati ta dauki dukkanin wani matakin daya dace domin tallafawa al’umma. To da farko dai ya kamata malamai su ci gaba da gaya wa al’umma wannan yanayi jarabawa ce daga Allah don haka ya kamata mu koma gare shi domin ya magance ta domin babu mai kawo karshen wannan matsala sai Allah, mu kuma mutane ya kamata mu kyautata aiki kuma mu taimakawa ‘yan uwan dake cikin wani hali ba wai sai gwamnati kadai ba, kowa ya taimaka da abun da zai iya. To ya kamata su ji tsoron Allah su sani babu kawo karshen wannan matsala sai Allah, don haka bai kamata su saba masa domin neman mafitar komawa gare shi da kuma kyautata aiki da taimakawa juna sune mafita a cikin wannan matsala, su kuma maza da suke irin wannan halin ya kamata su ma su ji tsoron Allah su sani Allah zai tambaye su akan wannan hali da suka jefa iyalan su, daga nan nake addu’ar Allah ya kawo mana karshen wannan matsala don Alfarmar Annabin rahama (S.A.W).
Sunana Yareema Shaheed (Abou Hashmat), Daga Jihar Katsina:
Tabbas tsadar rayuwa ya ta’azzara a nageriya wajen hauhawan kayan abinci, mutane suna cikin mawuyacin hali. Gwamnati ta ji tsoron Allah ta sani duk halin da al’umma suke ciki Allah zai tambayeku akan shugabancinku don haka dan Allah ku kara jajircewa wajen tausaya wa Al’umma da ku ke mulka. Hakuri da juriya domin komai ya yi farko zai yi karshe, ba kanmu ne farau ba domin ko Annabawa an jarabcesu da yunwa, Allah ya kawo mana sauki. Mata da Maza ku ji tsoron Allah domin Allah na tare da masu hakuri da kaddara mai kyau da akasinsa mu tsarkake zuciyarmu.
Sunana Comared Umar Baban Yaya Sabongida Karamar Hukumar Kafin Hausa A Jihar Jigawa:
Tabbas! akwai takaici matuka kan yadda ‘yan mata da kuma matan Aure ke jefa rayuwar su cikin irin wannan hali, na farko suna da karamin karfi, na biyu kuma ba suda wata hanya da za su iya taimaka wa kansu, don haka kamata yayi a rinka duba halin da mata ke ciki, domin taimakon rayuwarsu, sanya kansu kuma cikin rayuwar zinace-zinace ba yin kansu bane dole ce kowa ya sani sai dai fatan Allah ya kawo mafuta. Ta bangaren guduwa kuma da maza ke yi wa iyalansu abin dubawa ne, ganin matsi da ake ciki. Shawara ta daya ce a wannan bangare shi ne; a rinka Addu’oi domin samun saukin wannan hali da ake ciki, guduwa ba tawakkali ga ubangijin halitta ba ce. Gwamnati ba wai kira zamu yi a gare ki kan halin da muke ciki ba, sai dai mu kara sanar miki halin da al’umma ke ciki, domin wallahi gaba kadan da yawa daga cikin talakawanki za su rasa rayukansu ta bangaren yunwa, takaici, tunani da dai sauransu. Jama’a muna fatan za mu dukufa wajan yi wa kasar mu da kanmu addu’oi domin hakan shi ne kawai mafuta a gare mu fatan Allah ya fitar damu lafiya.
Sunana G Daniel Abarshi, Daga jihar Bauchi Tafawa Balewa LGA:
A gaskiya in zamu duba rayuwarmu na baya da kuma yadda muke a yanzu zamu ga muna da matukar bambanci yawancinmu mutane a yau muna buya ne a bayan wayonmu yawanci a yanzu mutane koda kuwa mun yi noma sai ka ga munata saida amfanin gonarmu, akan wata bukatar da bai taka kara ya karya ba, sai ka ga muna ta saida amfanin da zai rufa mana isiri yadda ma za mu iya taimakawa wani, ko kuma ka ga muna ta sayarwa ‘yan kasuwa amfaninmu su kuma sai su yi ta ajiyewa lokacin da muka rasa sai su futo mana da shi. Suna sayar mana da tsada wanda ni ina ganin laifinmu ne hakan. Allah ya kyauta ni kiran da zan yi wa gwamnati da ‘yan kasuwarmu akan dan Allah mu rika tausayawa al’umma in ka san ka samu riba a baiwa masu saya, dan wallahi wasu abincinma basa samu su ci. Amma in ka yi masa sauki koda kuwa ka ciri ba akansu shi zai ga ba shi da masoyin daya wuce kai har addu’oi za su dinga yi maka.