Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya kaddamar da kwamitin sa ido kan rabon kayayyakin agaji na musamman a Tudun Biri domin tabbatar da gaskiya da adalci wajen rabon kayayyakin.
Kwamitin zai tabbatar da cewa an raba kudaden cikin adalci domin farantawa wadanda suka tsira da rayukansu da kuma iyalan wadanda suka rasa rayukansu da dukiyoyinsu a wani mummunan harin bam da sojoji suka kai kauyen Tudun Biri da ke Karamar Hukumar Igabi a ranar Lahadi, 3 ga Disamba, 2023.
- Gwamna Uba Sani Ya Kaddamar Da Sabon Titin Sanga-Kafanchan Mai Tsawon Kilomita 18
- Bankwana Da 2023: Rasuwar Darakta Aminu S Bono
A cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamnan, Muhammad Lawal Shehu ya fitar, an bayyana cewa, gwamnan ya nuna yabawa da irin matakan da hukumomin da abin ya shafa suka dauka biyo bayan afkuwar lamarin a jihar.
“Muna so mu tabbatar da cewa, gudunmawar da aka bayar ta isa ga ainihin wadanda lamarin ya shafa. Dole me mu sa Ido kan yadda za a gudanar da kasafin gudunmawar domin tabbatar da aikin cikin hanzari da inganci,” in ji Gwamna Sani.