Turkiyya na karbar bakuncin taro tsakanin manyan jami’an diflomasiyyar kasashen Musulmi da nufin samar da mafita ga makomar Gaza dai-dai lokacin da ake ganin yadda Isra’ila ke ci gaba da karya ka’idojin yarjejeniyar da aka kulla da ita a wani yanayi da shugaba Recep Tayyib Erdogan ke rokon Hamas kan ta tabbata ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar duk da tunzuri daga Isra’ilan.
Ministocin wajen kasashen Saudiya da Katar da kuma Daular Larabawa baya ga Jordan da Pakistan da kuma Indonesia ne suka hallara a birnin Santanbul bisa gayyatar ministan harkokin wajen Turkiyyan Hakan Fidan da nufin tattaunawa kan Gaza, yankin da ya yi fama da yakin shekaru 2 kuma tsagaita wutar da aka yi karkashin yarjejeniyar da aka cimma a ranar 10 ga watan Oktoba ke fuskantar barazana daga Isra’ila, bayan da kasar ta Yahudu ta ce wasu Falasdinawa na kaiwa Sojojinta hari wanda ya sanyata dawo da hare-hare a Gazan.
- An Bukaci Manoma Su Rungumi Tsarin Noma Mai Jure Wa Sauyin Yanayi
- Yadda PDP Ta Yi Asarar Kudancin Kaduna
Dukkanin wakilan kasashen da suka hallara a birnin na Santanbul na cikin wadanda suka yi taro da Donald Trump cikin watan Satumba gabanin shugaban na Amurka ya fitar da daftarin kudirinsa kan yarjejeniyar ta Gaza.
Ministan wajen na Turkiya ya ce kasar shi na neman goyon bayan wadannan kasashe da nufin mara baya ga Falasdinawa wajen ganin sun karbi ragamar iko da dukkanin yankunansu na gabar ruwa baya ga tsayuwar daka kan sha’anin tsaron yankinsu ba tare da shigar wasu kasashe ba.
Ko a karshen mako sai da Turkiyan ta karbi bakuncin jagoran Hamas Khalil al-Hayyan inda shugaba Erdogan ke cewa bisa dukkan alamu, Hamas na mutunta yarjejeniyar da aka kulla yana mai cewa Isra’ila ke son wargajewarta.
Fidan ya ci gaba da cewa akwai bukatar fara aiwatar da kudirin da aka cimma yayin taron kasashen Musulmi na OIC da kuma Arab League dangane sake gina Gaza don karfafa da kuma tallafar rayuwar dimbin Falasdinawan da Isra’ila ta tagayyara.














