Dattijon kasa kuma tsohon babban hafsan soji, Janar Theophilus Danjuma (rtd), ya bukaci dukkanin hafsoshin tsaro da su kawo karshen ‘yan bindiga tare da mayar da kasar kan turbar zaman lafiya.
Babban hafsan soji mai ritaya, wanda ya yi tir da yadda ake ci gaba da yin garkuwa da mutane da kashe-kashe, ya ce babu “wani uzuri” na ci gaba da ta’addanci da ke addabar kasar.
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 4 A Birnin Gwari Da Giwa Bayan Kubutar Da Mutane 20 A Kaduna
- Ambaliya: Muna Da Bayanan Fursunonin Da Suka Tsere A Maiduguri — Hukuma
Ɗanjuma ya bayyana haka ne a wajen taron kaddamar da wani littafi mai suna: “Big Boots: Lessons from my Military service”, wanda Solomon Udounwa, Manjo-Janar na Sojojin Nijeriya mai ritaya ya rubuta, a Abuja.
Ya ce, “matsala ta daya a Nijeriya, ita ce tsaro. Dole ne mu kawo karshen wannan annoba, ta kashe-kashe da garkuwa da mutane da ke faruwa a kasarmu da wuri. Ku da kuke kan yi wa kasa hidima, ba ku da uzuri!”
Janar din haifaffen Jihar Taraba, wanda shi ne shugaban taron, ya yaba da kyawawan dabi’un marubucin da kuma jajircewarsa a fagen aikin soja.
Da yake mayar da martani kan tuhumar Danjuma, babban hafsan hafsoshi, Janar Christopher Musa, ya ce, sojoji a tsaye suke kuma suna aiki tukuru domin dawo da zaman lafiya a fadin kasar.
Musa ya jaddada cewa, sojojin kasar za su ci gaba da kiyaye kimar aiki da ɗaga darajar aikin soji a faɗin kasar kamar yadda aka san su.