Dan takarar gwamna a jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana mataimakiyar gwamnan jihar Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe a matsayin abokiyar takararsa a zaben gwamna na 2023.
Sani wanda ke wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa a halin yanzu, ya bayyana hakan ne a shafin sa na Twitter da aka tabbatar a daren ranar Litinin.
Kamar yadda Uba Sani ya rubuta: “Bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a jihar Kaduna, ina mai farin cikin sanar da cewa na zabi mai girma Mataimakiyar Gwamna, @DrHadiza Sabuwa Balarabe a matsayin abokiyar takarara a zaben gwamna na 2023 a jihar Kaduna.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp