Hukumar Uefa ta dage dukkan wasannin da aka shirya yi a Isra’ila a cikin makwanni biyu masu zuwa sakamakon karuwar tashe-tashen hankula a kasar.
Sama da ‘yan Isra’ila 600 ne aka kashe a hare-hare daga Gaza tun ranar Asabar, in ji gwamnati.
- UEFA Champions League: Abinda Ya Kamata Ku Sani Akan Wasan Real Madrid Da Napoli
- UEFA Champions League: Yaushe Za A Sauya Fasalin Gasar?
Uefa ta ce wasan da Isra’ila za ta buga da Switzerland a ranar Alhamis na daga cikin wasannin da aka dage bisa la’akari da yanayin tsaro.
Hukumar kwallon kafar Turai ta ce za a shirya sabbin ranakun da za’a buga wasannin.
Wasannin da aka jinkirta
12 ga Oktoba: Isra’ila da Switzerland
12 ga Oktoba: Isra’ila da Estonia
17 ga Oktoba: Isra’ila da Jamus
Uefa za ta ci gaba da sanya ido sosai kan lamarin kuma za ta ci gaba da tuntubar dukkan kungiyoyin da abin ya shafa kafin yanke shawara kan sabbin ranaku.
Zakarun gasar firimiya ta Isra’ila Maccabi Haifa na buga gasar cin kofin Europa a bana kuma za ta ziyarci Villarreal bayan an dawo hutun wasannin gida.