Rikici ya barke a karamar hukumar Fagge da ke jihar Kano a daren ranar Laraba a tsakanin wasu masu sha’awar kallon kwallon kafa, sakamakon wasan daf da na kusa da na karshe tsakanin Real Madrid da Arsenal a gasar cin kofin zakarun Turai (UEFA), inda Arsenal ta fitar da Real Madrid daga gasar.
Rikicin ya samo asali ne sakamakon kashin da Real Madrid ta sha a hannun Arsenal da ci 1-2, inda Arsenal din ta yi nasara da jimillar ci 5-1 a wasannin biyu wanda hakan ya sa za ta buga wasan na kusa da na karshe a karon farko cikin shekaru 16 a gasar cin kofin zakarun Turai cikin shekaru 16.
- Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Taron Ƙarawa Ma’aikatan Jinƙai Sani A Jihar Kano
- Arsenal Ta Yi Waje Rod Da Real Madrid Daga UEFA
Sakamakon ya haifar da bacin rai a tsakanin wasu magoya bayan kungiyar ta Real Madrid, inda magoya bayan kungiyoyin biyu suka yi arangama da juna bayan tashi daga wasan, wani faifan bidiyo da wani mai amfani da shafukan sada zumunta Mustapha Muhd Gujba Banker ya wallafa a Facebook ya dauki hankulan jama’a, a cikin faifan bidiyon, an ga wasu gungun matasa wadanda aka bayyana a matsayin magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa guda biyu, suna musayar naushi, suna jifan juna, da kuma yi wa juna ihu.
An tabbatar da cewa, tashin hankalin ya barke ne jim kadan bayan da alkalin wasa ya busa tashi daga wasan, kawo yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance da rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta fitar har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto a safiyar ranar Alhamis, kuma kawo yanzu babu tabbacin ko an samu raunika a yayin rikicin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp