Ukraine da Amurka sun cimma matsaya kan tsarin kulla yarjejeniyar tattalin arziki mai fadi da za ta hada da samun damar mallakar ma’adanan karkashin kasa da babu su a duniya, in ji wasu manyan jami’ain Ukraine uku.
Jami’an, wadanda ke da masaniya kan lamarin, sun yi magana bisa sharadin a sakaya sunayensu saboda ba’a ba su izinin magana a bainar jama’a ba.
- Noman Dabino: Jigawa Ta Yi Hadaka Da Saudiyya
- CBN Ya Umarci Daraktocin Bankuna Su Mayar Da Bashin Da Suka Karba Ko Su Yi Murabus
Daya daga cikinsu ya ce Kyib na fatan sanya hannun kan yarjejeniyar don tabbatar da ci gaba da bayar da tallafin sojin Amurka da Ukraine ke bukata cikin gaggawa.
Da yake magana da manema labarai a ofishin shugaban kasa, Donald Trump, ya ce ya ji cewa Zelenskyy na zuwa, ya kuma kara da cewa “babu komai a wurina, idan ya so, kuma yana iya sanya hannun tare da ni.”
Za’a iya sanya hannun kan yarjejeniyar nan da ranar Juma’a mai zuwa kuma an shirya tsaf game da tafiyar shugaban Ukraine Bolodymyr zuwa Washington don ganawa da Trump, a cewar daya daga cikin jami’in Ukraine.
Wani jami’in ya ce yarjejejeniyar za ta ba da dama ga Zelenskyy da Trump su tattauna batun ci gaba da bayar da tallafin soji ga Ukraine, dalilin da ya sa Kyib ke son kammala yarjejeniyar.
Trump ya kwatanta wannan matsaya da aka cimma a matsayin “babbar yarjejeniyar,” wacce za ta kai ta tiriliyan na daloli.
A wani labarin kuma, Kasar Ukraine ta bayyana cewar hare-haren da Rasha ta kai wa garuruwan dake kusa da filin daga a gabashin kasar sun hallaka akalla mutum 5 tare da raunata wasu 8 ‘yan sa’o’i bayan wani mummunana harin jirgi mara matuki kusa da birnin Kyib.
Gagarumin ruwan wutar da jiragen saman Rasha marasa matuka suka kai cikin dare sun hallaka mutum 2 a kusa da birnin Kyib, ciki har da wata ‘yar jaridar Ukraine, kamar yadda kafar yada labaran da take yiwa aiki ta bayyana.
‘Yan jaridar dake yi wa kamfanin dillancin labarai na Afp aiki a Kyib sun ji karar fashewa bayan da rundunar sojin saman Ukraine ta ce Rasha ta yi barin wuta da jirage sama marasa matuka 177 masu nau’uka daban-daban kan wuraren da ta kai wa hari a fadin kasar.
Dakarun Rasha na kokarin kwace iko da garin Kostyantynibka kuma sun tsananta wajen yin luguden wuta akan sansanonin farar hula dake yankin gabashin Donetsk, wanda fadar Kremlin ke ikrarin cewa wani bangare ne na Rasha.
“An hallaka akalla mutum 5 kana an raunata wasu 8 a hare-haren da ake kai wa Kostyantynibka,” kamar yadda gwamnan yankin Donetsk Badim Filashkin ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.
Hare-haren wata shaida ce ga karin wahalar da dakarun Ukraine ke sha a hannun rundunar sojin Rasha wacce ta ninkasu kudi da kayan aiki da kuma yawan dakaru a fadin fagagen daga.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp