Jam’iyyar APC ta bayyana umurnin wata babbar kotun jihar Kano da ta tabbatar da dakatar da shugabanta na kasa, Dakta Abdullahi Ganduje a matsayin rashin sanin iya aiki, inda ta ce, ba za ta amince ko mutunta umarnin ba.
Mai baiwa jam’iyyar APC shawara kan harkokin shari’a, Farfesa Abdulkarim Kana ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan shugabannin jam’iyyar APC na unguwar Ganduje ta jihar Kano sun ziyarci shugaban jam’iyyar na kasa a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja a ranar Laraba.
- Shari’ar Zargin Karkatar Da Dukiyar Al’umma: Ganduje Da Iyalansa Ba Bu Wanda Ya Halarci Kotu
- Ko Manufar Kariyar Ciniki Za Ta Kai Ga Bunkasa Manasana’atun Da Abin Ya Shafa Na Kasashen Turai?
Kana ya kuma ce, shuwagabannin jam’iyyar a matakin unguwar tuni suka garzaya gaban majalisar shari’a ta kasa (NJC) domin gabatar da kara a kan alkalin babbar kotun Kano da ya yanke hukuncin domin a ja masa kunne.
Kana ya kara da cewa, mutanen da ke da hannu a yunkurin dakatarwar ba ‘ya’yan jam’iyyar APC ba ne, ba kuma shugabannin jam’iyyar ba ne a Unguwar Ganduje.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp