Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana wa masu zuba jari na ƙasashen waje cewa Nijeriya na da damar zuba jari mai darajar sama da Dala Biliyan 200 a fannin makamashi.
Ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa da Ƙungiyar Kasuwanci ta Ƙasa da Ƙasa (Business Council for International Understanding – BCIU) ta shirya a birnin New York, Amurka, gabanin taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80.
- Jihar Kogi Na Cikin Fargaba Yayin Da Kogin Neja Da Benuwe Suka Tumfatsa
- Majalisar Dattawa Ta Buɗe Ofishin Sanata Natasha
Shettima ya ce Nijeriya na buƙatar haɗin gwiwa da abokan hulɗa domin cin gajiyar wannan dama, musamman a fannonin makamashi na zamani. Ya ce Nijeriya na da mai da iskar gas mafi yawa a Afirka, da kuma hasken rana mai ƙarfi fiye da ƙasashe da dama a nahiyar.
Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa tuni gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ɗauki manyan matakai na gyara tattalin arziki, ciki har da cire tallafin man fetur, haɗa farashin musayar kuɗi, da kuma sabunta tsarin haraji da kwastam.
Ya ƙara da cewa waɗannan sauye-sauye sun fara samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari, inda ya nuna cewa manyan kamfanonin tantance darajar kuɗi irin su Fitch da Moody’s sun ɗaga matsayin Najeriya saboda ingantattun manufofi da ƙaruwar ajiyar kuɗi.