Hukumar kula da yawon bude ido ta duniya (UNWTO) ta yaba da muhimmancin sake bude kasar Sin ga yawon bude ido, ganin yadda kasar take da matukar muhimmanci ga kasuwar yawon bude ido ta duniya.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta UNWTO ta fitar jiya Alhamis, ta bayyana cewa, sake bude kasar Sin yana wakiltar farfado da harkokin yawon bude ido a duniya, bayan matsala mafi muni da bangare ya tsinci kansa a tarihi.
Alkaluman hukumar na nuna cewa, a shekarar 2019 kafin barkewar annobar COVID-19, kasar Sin ta kasance babbar kasuwar yawon bude ido a duniya. ‘yan yawon bude ido na kasar Sin sun yi balaguro na kasa da kasa da ya kai miliyan 166, inda suka kashe dalar Amurka biliyan 270, mafi yawansu a wuraren da kasashe masu tasowa ke ci gaba da samun bunkasar tattalin arziki. (Mai fassarawa: Ibrahim)