Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire, JAMB ta umurci jami’an tsaro da duk masu cibiyar zana jarrabawa (CBT) da su cafke duk iyayen da suka gani kusa da cibiyar a lokacin gudanar da jarrabawar ta 2024 (UTME).
Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta JAMB, Dr. Fabian Benjamin, ya sanya wa hannu a ranar Alhamis, ta ce an bayar da umarnin ne a taron karshe na masu CBT, wanda aka gudanar a ranar Laraba, 17 ga Afrilu, 2024.
- Tirka-tirkar Daliba Ejikeme Mmesoma: Masani Ya Tona Asirin Yadda Ake Sauya Sakamakon JAMB Na Bogi
- NDLEA Ta Kona Kilo 304,436 Tare Da Lita 40,042 Na Haramtattun Kwayoyi Da Aka Kama A Legas Da Ogun
JAMB ta bayyana cewa, umarnin ya zama dole biyo bayan kutsawar da wasu iyaye suka yi a lokutan zana jarrabawar da ta gabata.
A cewar magatakardar hukumar ta JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, “duk iyayen da suka ki bin wannan umarnin, ba kawai za a kama su ba ne, za a haramta wa ‘ya’yansu shiga zana jarrabawar.”